4 Janairu 2022 - 13:55
An Gudanar Da Many-Manyan Tarurrukan Juyayin Shahadar Sulaimani A Kasashe 6

A dai dai lokacinda ake cika shekaru 2 da kissan jagororin yaki da ‘yan ta’adda a duniya, wato Kasim Sulaimani da Mahdi Al-muhandis, da abokan tafiyansu, an gudanar da manya manyan tarurruka a kasashe 6 a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa a birnin Mosco babban birnin kasar Rasha an Janar Ughani Goonchoruv wakilin sojojin Rasha a taron ya bayyana cewa kasar Rash aba zata manta da taimakon da Shahid Qasim Sulaimani ya yiwa sojojin Rasha a lokacin da ‘yan ta’adda suka mamaye kasar Siriya ba.

An gudanar da irin wannan tarurrukan a kasashen Iraki a wurin da aka kashe shahidan. Har’ika yau a kasashen Yemen Siriya da kuma Lebanon an kudanar da irin wadannan tarurruka.

Daga karshe a yankin Gaza Falasdinawa sun gudanar da gagarumin taro don tunawa da wadannan shahidai.

342/