Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin sakon sabuwar shekara kungiyar kare hakkin musulmi a Najeriya ta bayyana fatan ganin an kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar.
A cikin sakon, babban daraktan kungiyar kare hakkin musulmi a Najeriya MURIC Ishaq Akintola ya ce ‘yan Najeriya su yi godiya su daina duk wani abu na laifi, yada labaran karya da kalaman nuna kiyayya, tare da rungumar zaman lafiya a tsakanin dukkanin al’ummomi na kasar.
Ya ce “Muna gargadin cewa yada labaran karya, kalaman kiyayya da yin duk wani abu da zai iya tayar da hankali, da rusa kasa, wannan salo ne na yaudarar ‘yan Najeriya musamman matasa,” in ji daraktan
Ya ce a duk lokacin da aka samu irin hakan, to abin da zai biyo baya shi ne ko dai rikicin kabilanci ko kuma na addini wanda ke haifar da kashe-kashe da lalata dukiyoyi na kasa da kuma na al’umma.
342/