1 Janairu 2022 - 16:35
​Cibiyar Musulunci Ta Azhar Ta Mika Sakon Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Miladiyya Ta 2022

Sheikh Ahmed al-Tayyib, Sheikh al-Azhar, ya wallafa a shafinsa na Twitter yana taya kiristoci a fadin duniya murnar Kirsimeti da kuma shiga sabuwar shekara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin wani sako ga Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya bababn malamin na Azhar yana cewa; "Paparoma Tawadros II", shugaban Kiristoci 'yan Koftik a Masar; Justin Welby, Archbishop na Cocin Canterbury; Shugabannin coci-coci da na Kirista a Gabas da Yamma muna taya ku murnar shiga sabuwar shekara ta 2022.

Sheikh Ahmed al-Tayyib ya wallafa sakon taya murnar ne a shafukansa na sada zumunta da harsuna shida da suka hada da Ingilishi da Larabci da Faransanci da Italiyanci da kuma Turkiyya.

Ya ce “Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba mu zaman lafiya da soyayya da ‘yan uwantaka a duniya, ya kuma tseratar da mu daga yaki da kiyayya,” inji shi.

342/