25 Disamba 2021 - 14:16
Hadi Al-Amiri Ya Yi Gargadi Kan Rashin Janyewar Dakarun Kasashen Waje Daga Iraki

Shugaban kawancen Fatah ya ce: Idan dakarun kasashen waje ba su fice daga Iraki ba, kasar za ta kasance cikin rashin kwanciyar hankali.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, Hadi Al-Amiri shugaban gamayyar kungiyar Fatah ta kasar Iraki a wata ganawa da yayi da jakadan kasar Japan Kotaro Suzuki ya yi gargadi game da rashin janyewar sojojin kasashen waje daga kasar idan har karshen wannan shekara, ba su fita ba, kasar nan za ta zama cikin rashin kwanciyar hankali.

Shugaban kawancen na Fatah ya ci gaba da cewa: Matsayinmu kan kasancewar dakarun kasashen waje a fili yake domin sune matsalar hukumar mu.

Al-Amiri ya kara da cewa: Idan har Iraki na bukatar masu ba da shawara daga kasashen waje don neman ilimi da tuntubar juna, to dole ne ta kasance daidai da kundin tsarin mulkin Iraki da kuma dokokin da ake da su a halin yanzu, tare da bayyana gaskiya.

Yayin da yake amincewa da muhimmiyar rawar da Japan ke takawa a yankin, shugaban gamayyar kungiyoyin Fatah ya yaba da matsayin Tokyo na goyon bayan zaman lafiyar Iraki da kuma karfafa tafarkin dimokuradiyya.

A nasa bangaren, Suzuki, kan rawar da Irakin ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, ya kuma ce kasarsa na ci gaba da taimakawa Irakin a dukkan fannoni.

Jakadan na Japan ya kara da cewa: Duniya na bibiyar abubuwan da ke faruwa a Iraki, kuma tana sa ran za a warware rikicin siyasar Iraki ta hanyar demokradiyya.

342/