Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Wanan matakin yana zuwa ne a wani yunkurin na buunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasasen guda 3 wato Eco, da kuma karyar takunkumi Amurka da neman mayar da kasar iran saniyar ware
Kasahen guda Ukku sun kaddamar da safarar jiragen kasa na dakon da kwantenoni tun a shekara ta 2009 , sai dai gwaji kwai aka fara amma bai fara aiki gadangadan ba, kuma wannan tsohon mafarki ne da kasashen 3 suka dade suna yi daya ya zamo gaskiya yanzu, wanda hakan zai taimakawa kasashen 3 wajen yin aiki tare da tabbatar da daidaito da zaman lafiya a yankin
Kasar Amurka tan a amfani da siyasar matsin lamba kan kasar Iran don mayar da ita saniyar ware, da kuma hana yin duk wani nau’in huldar kasuwanci na kasa da kasa da kasar iran. Sai dai Iran ta nuna wa Amurka a aikace cewa ba za ta sabu ba bindiga a ruwa ba za ta iya hanata yin hulda da makwabta ba,
342/