18 Disamba 2021 - 15:22
​Falasdinu Ta Yi Maraba Da Kudirin MDD, Na Tabbatar Da ‘Yancin Cin Gashin Kai Ga Al’ummar Falasdinu

Falasdinu, a ranar Juma’a ta yi maraba da kuri’ar da majalisar Dinkin Duniya ta kada na amincewa da wani kudiri da ke tabbatar da ‘yancin cin gashin kai ga al’ummar Falasdinu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Amincewa da kudirin wani martanin duniya ne kan Isra’ila game da laifukan da take aikatawa ga al’ummar falasdinu, inji ministan harkokin wajen Falasdinu Riyad Al’Maliki.

kimanin kasashe 168 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin na ranar Alhamis. Saidai Amurka da Isra’ila sun kada kuri’ar kin amincewa da kudirin, yayin da wasu kasashe goma suka kauracewa kada tasu kuri’a.

Falasdinu ta kuma bukaci kasashen duniya dasu ci gaba da tallafawa al’umma falasdinu su gane ‘yancinsu na cin gashin kai ciki har da kafa kasa mai cin gashin kanta.

342/