18 Disamba 2021 - 15:21
​MDD Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Rikicin Yankin Tigray Na Habasha

Kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da kafa wani kwamitin kasa da kasa domin binciken zargin aikata ba daidai ba yayin rikicin yankin Tigray na Habasha.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Kwamitin zai binciki dukkan bangarorin dake da hannu a rikicin yankin na Tigray kan aikata ba daidai ba, kamar yadda wani bangare na mambobin kwamitin suka amince a zamansu na jiya Juma’a, saidai babu wata kasa daga Afrika da ta goyi bayan kudirin.

Kwararu kimanin ashirin da suka hada da sojoji, masu shari’a, ‘yan sanda da likitoci, kuma zasu yi aiki na tsawon shekara guda da za’a iya tsawaitawa idan bukatar hakan ta taso.

Kwamitin na MDD, an dora masa nauyin gabatar da rahoton binciken ga kwamitin kare hakkin dan adam a Geneva, da kuma babban zauren MDD na birnin New York.

342/