14 Disamba 2021 - 18:31
Iran. Isra’ila Ce Mikiyar Musulmi Na Daya A Duniya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khadib Zadeh ya bayyana cewa haramtacciyar kasar Isar'ila (HKI) ce makiyar musulmi ta farko a duniya kuma duk kokarinda shuwagabnnin kasashen larabawa zasu yi na kauda hankalin musulmi daga mummunan halin da al-ummar Falasdinu take ciki ba zai sami nasara ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto KhadibZadeh yana fadar haka a jiya Litinin, a dai dai lokacinda firai ministan HKI Naftali Bennett ya isa birnin Abudabi na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ziyara irinta na farko wanda babban jami’an HKI ya kawo kasar.

Naftali Bennett ya gana da sarkin kasar UAE, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a birnin Abudabi. Kuma ziyarar tana zuwa ne a dai dai lokacinda ake cika shekara guda da samar da huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu a shekarar da ta gabata.

342/