13 Disamba 2021 - 14:05
Iran Ta Shawaraci Kasashen Turai Da Su Sa Basira A Tattaunawar Da Ake Yi A Biyanna

A wata hira da gidan talbijin din Al-mayadeen yayi da babban mai shiga tsakani na kasar Iran a tattaunawar da ake yi na neman cirewa Iran takunkumi a Biyanna Ali Bagheri Kani ya fadi cewa: “ Iran ta yi amfani da tafarkin hankali da tunani a tattaunawar da ake yi da zai kai ga cin nasara

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Ya kara da cewa Iran ta shiga tattaunawar ce da kyakkyawar Niyya kuma ta yi amfani da hanyoyin da za su karfafa daya bangaren wajen amfani da hikima da zurfin tunani a wajen tattaunawar

Da yake bayani game da makircin da isra’aila take kullawa na ganin tattaunawar bata yi nasara ba y a fadi cewa: “Isra’ila tana kokarin yin zagon kasa daga wajen dakin taron yadda zai yi tasiri a sakamakon tattaunawar da za’a fitar daga karshe,

Ya ce a tattaunawar zagaye na 7 da aka yi Iran ta kaddamar da daftarin kuduri guda 2 , na farko ya mayar da hankali ne game da batun cire mata dukkan takunkuman da aka kakaba mata, na biyu kuma game da aikace-aikacen ta na makamashin nukiliya na zaman lafiya,

Iran ta mayar da hankali kan batun cire mata takunkumi , kuma ta jaddada cewa ba za ta amince da wata sabuwar Yarjejeniya da ta wuce wadda aka cimma a shekara ta 2015 ba.

342/