Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Cheikh Tahnoun bin Zayed, na wannan ziyarar ce bisa gayyatar sakaren majalisar tsaron kasa ta Iran.
Yayin ziyarar tasa an tsara zai gana da takwaransa na Iran, Admiral, Ali Shmkhani, da kuwa wasu manyan jami’an kasar ta Iran.
Karfafa alaka da kuma tattauna halin da ake ciki a baya bayan nan a yankin na daga cikin ajandar ziyarar ta Cheikh Tahnoun bin Zayed na UAE a birnin na Tehran.
Wannan kuma manuniya ce ta alkawarin da sabon shugaban kasar ta Iran, Ebrahim Ra’asi ya dauka na fifita karfafa alaka da kasashe makobtan kasarsa.
Iran da UAE, na da sabani akan batutuwa da dama da suka shafi yankin, musamman batun Siriya da Yemen, amma kuma suna dasawa sosai ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci.
342/