Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Sama da ‘yan kasar dubu 960 ne da suka cancenci zabe ke kada kuria’a a zaben, wanda shi ne kuma na farko tun bayan mulkin tsohon shugaba Yahya Jammeh.
‘Yan takara shida ne ke fafatawa a zaben da ake wa kallon zakaren gwajin dafi ga danyar demukuradiyyar kasar dake yankin yammacin Afrika.
Daga cikin ‘yan takaran har da shugaba mai barin gado Adama Barrow da kuma tsohon mataimakinsa Ousainou Darboe, kana madugun ‘yan adawa na kasar.
Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya bukaci dukkan bangarori na al’ummar kasar dasu bada himma wajen yin zabe mai sabta kuma cikin lumana.
342/