3 Disamba 2021 - 16:10
Kotu Ta Bayar Da Umarnin Maida Dan Gaddafi A Cikin ‘Yan Takaran Zabe

Wata kotun daukaka kara a birnin Sebha da ke kudancin Libya a ranar Alhamis ta bayar da umarnin mayar da Seif al-Islam Gaddafi, dan tsohon shugaban kasar, a cikin jerin 'yan takara da zasu fafata a zaben shugaban kasar da za a yi ranar 24 ga watan Disamba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shi dai dan Muammar Gaddafi ya daukaka kara a gaban wannan kotu kan matakin da hukumar zaben kasar ta dauka na kin amincewa da takararsa saboda tanade-tanaden doka.

Hukuncin kotun ya faramtawa magoya bayan Seif Al Islam rai a kotun da ke Sebha, dake da tazarar kilomita 650 kudu da birnin Tripoli.

An dai zargi dan tsohon shugaban kasar da cin zarafin bil adama a lokacin guguwar neman sauyin data yi awan gaba da mulkin mahaifinsa a shekarar 2011, kuma tun lokacin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nemansa ruwa a jallo.

342/