Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Rahoton ya kara da cewa, falasdinawa 133 ne suka ji wa rauni sannan sun kama falasdiawa 199 a yankin yamma da kogin Jordan kadai a cikin watan.
Cibiyar ta kara da cewa a cikin watan Nuwamban da ya gabata HKI ta rusa gidaje da wuraren kasuwanci na falasdiawa har 54. Banda haka yahudawa wadanda ba jami’an tsaro ba sun farwa falasdinawa har sau 56 a cikin watan.
Har’ila yau yahudawa 1,629 suka keta hurumin masallacin al-aksa suka shiga cikinsa sanna suka kori falasdiawa 10 daga masallacin. Sai kuma a cikin watan da ya gabata ne gwamnatin HKI ta kuduri anniyar gida gidaje wa yahudawa a filin saukar jiragen sama na Qudus wanda ake kira Qalandiya har guda 11,000.
342/