Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zahra Ershadi tana fadar haka a gaban kwamiti na 3 na kwamkin tsaro a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, ganin Irin kasashen da suka gabatar da bukatar a samar da wannan kuduri don bata sunan Iran a duniya, wato kasashen Canada, Amurka da Isra’ila da sauran kasashen yamma, ba abin mamaki bane.
Don wadanan kasashe su ne a gaba a duniya wajen kashe yara kanana a kasar Falasdinu da suka mamaye, ko kuma kasar Canada inda aka yi wa yara kanana ‘yan makarantar kwana ‘yan asalin kasar piyade, sannan a kashe su a binne a kaburbura na gama gari.
Don haka Iran bata amince da wannan kudurin ba, don siyasa ce aka sanay ciki ba gaskiyan abinda yake kasa ba ne.
Banda haka Ershadi ta kammala da cewa kasar Iran tana bakarta na mutunta dukkan kudurrin kasa da kasa da suka shafi kare hakkin bil’adama.
342/