Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A wani bayanin da ya yi a gidan talabijin, Haftar ya ce ta hanyar zabe ne kawai za’a shawo kan rikicin.
Furucin na Janar Haftar, na zuwa ne, kwana daya bayan da dan tsohon shugaban kasar Mu’ammar Ghaddafi, Seif Al Islam, ya ajiye takardun takararsa a zaben shugaban kasar dake tafe na ranar 29 ga watan Disamba.
Takarar mutanen biyu na zuwa ne duk da bukatar da mai gabatar da kara na sojoji Mohamed Gharouda, ya yi inda ya nemi hukumar zaben kasar ta dakatar da takardun takarar Janar Haftar, ta kuma yi wasti da ta Seif al-Islam.
"Ana zargin Seif al-Islam da Khalifa Haftar da aikata laifuka” kuma dole a dakatar da bukatar takararsu har sai an kammala bincike,” kamar yadda babban mai gabatar da karar ya bayyana a cikin wata takarda da ya fitar.
342/