7 Nuwamba 2021 - 11:52
Firaministan Iraki, Ya Tsallake Rijiya Da Baya, A Wani Harin Jirgi Marar Matuki

Firayi ministan Iraki, Moustafa al-Kazimi, ya tsallake rijiya da baya a wani harin jirgi marar matuki da aka kai kan gidansa dake yankin Greeen zone a Badagaza a cikin daren jiya wayewar wannan safiya ta Lahadi, kamar yadda Ofishin firaministan ya sanar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jim kadan bayan firayi ministan ya fitar da wani sako a shafinsa na Twitter, inda yake cewa, ‘’ina cikin koshin lafiya, godiya ga Allah, sannan kuma ina kira ga dukkan bagarori dasu kai zuciya nesa’’

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sannan ba’a kai ga tantance irin ta’asar da harin ya haifar ba.

Kafin hakan dama wasu majoyoyin tsaro sun shaida cewa an kai harin rokoki guda biyu kan gidan firayi ministan Mustafa Al-Kazimi, a yankin mai cikakken tsaro dake tsakiyar babban binrin kasar wan ya kunshi ofishin jakadancin Amurka da kuma gine gine na gwamnati.

Bayanai daga kasar sun ce an baza jami’an tsaro a haraba da kuma gewayen inda lamarin ya faru.

Tuni Amurka ta yi tir da harin wanda ta ce na ta’addanci ne.

342/