2 Nuwamba 2021 - 14:41
Sudan: Akwai Fatan Za’a Sami Mafita A Rikicin Siyasar Kasar Nan Da ‘Yan Kwanaki

Masu shiga tsakani na ciki da wajen kasar Sudan suna kokarin ganin an fidda kasar daga rikicin siyasa wanda ya kai ga juyin mulkin da aka yi wa gwamnatin Adballah Hamduk a ranar litinin 25 ga watan Oktoban da ya gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a halin yanzu masu shiga tsakani na cik da wajen kasar suna kai kawo tsakanin shugaban juyin mulkin Janar Abdulfatta Alburhan da kuma firai ministan da aka tumbuke Abdallah Hamduk don warware rikicin siyasar da kasar ta fada cikin.

Jakadan MDD na musamman a kasar Sudan Volker Perthes na daga cikin masu shiga tsakani a rikicin siyasar kasar ta Sudan na baya-bayan nan. Perthes ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa firaiministan kasar wanda aka tumbuke kuma wanda yake zaman daurin talala a gidansa a halin yanzu, wato Abdullah Hamduk, ya bukaci sojojin su saki duk wadanda aka kama sannan su bar majalisar ministocinsa su koma bakin ayukansu, a wajensa shi ne kawai zai kawo karshen halin da ake ciki.

Wasu kuma suna bukatar a bawa Abdullah Hamduk damar kafa sabuwar gwamnati wacce zaka kunshi kwararru a ko wani fanni ne kawai. Wanda kuma zai kawo karshen gwamnatin rabon mukamai tsakanin jam’iyyun siya da kuma tsoffin kungiyoyin yan tawayen kasar.

Shekaru 2.5 kenan da zanga-zangan da ta hambarar da tsohon shugaban kasar Umar Hassan El-Bashir wanda ya mulki kasar har da tsawon shekaru 30, kasar Sudan ta sake shiga rikicin siyasa, bayan wani juyin mulki wanda Janar Burhan ya jagoranta a ranar litinin 25 ga watan Oktoban da ya gabata.

342/