Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bayan shafe kwanaki na tattaunawa game da rikicin diflomastiyan, shugaba Erdogan, ya fasa korar jakadun wadanda suka goyi bayan dan fafatukar nan Osman Kavala, da hukumomin Turkiyya ke tsare da tun cikin shekarar 2017, bisa zargin tada zaune tsaye da kuma yunkurin juyin mulki wa Erdogan.
Mista Erdogan, ya ce jakadun sun gane kuren su, tare da fatan cewa nan gaba zasu kara kiyayewa.
Sa’o’I kadan kafin hakan, ofishin jakadancin Amurka, ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa yana mutunta ayar doka mai lamba 41 ta yarjejeniyar Vienna kan huldar diflomatsiyya, wacce ta haramta duk wani shishigi a cikin lamuran cikin gida na wata kasa da take zamne.
Kuma ofisoshin jakadacin kasashen da batun ya shafa ciki har da Faransa da Jamus su ma sun sake wallafa irin sakon na tuwita.
342/