Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Sanarwar bayan taron da aka fiyar jiya Asabar wajen rufe taron ta bayyana halin da duniya ke ciki a yanzu da kuma kokarin ganin bayan wuce gona da iri na wasu kasashen duniya domin samar da zaman lafiya a fadin duniya."
Cimma wannan buri na bukatar hadin kan kasa da kasa na gaskiya, nesa ba kusa ba daga duk wani matsin lamba ko barazana, da kuma kawo karshen tsoma bakin wasu kasashe.
‘’Rikici, yaki da tashe-tashen hankula da ta'addanci a duniya, musamman a kasashen musulmi, yana nuna bukatar kasashen musulmi su dauki matakan gaggawa domin warware wadannan matsaloli a cewar sanarwar rufe taron."
342/