21 Oktoba 2021 - 16:05
​Kimanin Mata 100 Ne Aka Rantsar A Matsayin Alkalai Mata A Karon Farko A Kasar Masar

Babban jojin kasar Masar Mohammad Hossem El-din shi ne ya rantsar da Alkalai mata guda 98 da za su fara ayyuka a cibiyoyin shari’a na fadin kasar a wani biki da aka gudanar, inda ya yi marhabin da su kuma ya bayyana hakan a matsayin mataki mai muhimmanci sosai a cibiyoyin shari’a na jihohin kasar,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan yana zuwa ne bayan da shugaban kasar ta masar Abdul Fatah Al-sisi ya bukaci da sanya tare da damawa da mata cikin cibiyoyin shari’a dake jihohin kasar wanda yazuwa yanzu babu mata a cikinsu.

Wasu daga cikin alkalan sun nuna farincikinsu na ganin mafarkin da suka dade suna yi ya zama gaskiya na ganin an shigar da mata cikin cibiyoyin shari’a a kasar,

Matakin da Alsisi ya dauka a watan maris yazo ne bayan da kungiyoyin kare hakkin mata a kasar suka yi kira ga shugaban kasar da cewa lokaci yayi da za’a rike damawa da mata a cikin harkokin siyasa da na shari’a a fadin kasar.

342/