Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bayanai sun ce makami mai cin gajerin zango ne aka harba tun daga karkashin ruwa, zuwa tekun Japon.
Gwajin wanda shi ne irinsa na biyar tun daga watan Satumba, baa bun mamaki ne a cewar bayannan, saboda ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Seoul, ta bude wani baje kilin makamai lamarin da bai yi wa mahukuntan Pyangyang dadi ba.
Wannan shi ne gwajin makami na takwas da Koriya ta arewa ta yi tun daga farkon wannan shekara, a daidai lokacin da Amurka da kawarta Koriya ta Kudu, ke cewa suna bakin kokarinsu na komawa tattaunawa da gwamnatin Pyongyang.
342/