16 Oktoba 2021 - 17:31
​Sharm El-Sheikh: Masu Yawon Bude Ido Sun Fara Isa Kasar Masar Bayan An Sami Saukin Cutar Korona

A safiyar yau Asabar ce jirgin fasinja na farko daga kasar Burtaniya ya sauka a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar, bayan da gwamnatin kasar Burtaniya ta dage takunkumin hana zuwa kasashen da cutar korona ta fi yadawa a watannin da suka gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Daily News Egypt ta bayyana cewa Nabil Al-Mallah shugaban tashar jiragen sama na Sharm El-Sheikh ya tarbi fasinjoji na farko da suka isa kasar don yawon bude ido daga kasar Burtaniya tun watan yulin da ya gabata.

Jaridar ta kara da cewa Khaled Al-Anany ministan yawon bude ido na kasar Masar ya gana da jakadan kasar Burtaniya a kasar Masar makonni biyu da suka gabata kafin Burtaniya da dage hanin da ta yiwa ‘yan kasar zuwa Masar.

A cikin watan Yunin da ya gabata ne kasar ta Burtaniya ta sanya kasar Masar cikin jerin kasashen da ta hana ‘yan kasar zuwa saboda yadda cutar korona take yaduwa a cikinsu.

342/