12 Oktoba 2021 - 09:35
IRIB Ta Yi Sabon Shugaban Sashen Yada Labarai Na Duniya

Shugaban hukumar gidan talabijin da Radiyo na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Peyman Jebelli, ya nada Ahmad Norouzi a matsayin sabon shugaban sashen yada labarai na duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Dakta Jebelli ya ayyana Norouzi ga mukamin da ke kula da tashoshin harsunan waje na IRIB.

An dora masa alhakin kara karfafa sashen, kan bada labarai, da al'adu da addini da manufofin jamhuriyar musulinci ta Iran.

An haifi, Ahmad Norouzi a shekarar 1988, kuma dalibi ne na digiri na uku da ke karatun aikin gudanarwa a kafafen yada labarai a Jami'ar Tehran.

342/