Abdollahian ya bayyana hakan ne a yammacin jiya a birnin Beirut a yayin ziyarar da ya kai a kasar Lebanon, inda ya gana da manyan manyan jami’an gwamnatin kasar ta Lebanon, da suka hada da shugaban kasar Michel Aoun, da kuma Firayi minista Najib Miqati, da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Birri, gami da takwaransa na kasar ta Lebanon Abdullah Bou Habib.
Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana cewa, ganawarsa da manyan jami’an gwamnatin kasar Lebanon ta yi armashi matuka, domin kuwa an cimma abubuwa da dama a tsakanin bangarorin biyu wadanda za su mayar da hankali a kansu a halin yanzu.
Baya ga batun wadata kasar Lebanon da makamashi, day a hada da danyen man fetur gami da man dizel da kuma isakar gas, an cimma matsaya a kan gina wata tashar samar da wutar lantarki da Iran za ta yi a kasar Lebanon, inda za a fara aikin nan ba da jimawa ba, wanda zai dauki tsawon watanni 16 kafina fara cin gajiyar aikin.
Shugaban Lebanon Michel Aoun ya bayyana gamsuwarsa matuka kan gagarumin ci gaban da alaka tsakanin Lebanon da Iran take samu, kamar yadda shi ma a nasa bangaren Firayi ministan kasar ta Lebanon Najib Miqati ya bayyana farin cikinsa kan hakan.
Baya ganawa da jami’an gwamnati, Abdollahian ya gana da babban sakaren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah, da kuma wakilan kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa da ke Lebanon.



342/