Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kimanin ‘yan jarida 600 ne suka tattara bayanai kan wannan almundahana bayan sun gudanar da bincike a kasashen duniya 117, inda suka gano yadda attajirai da ‘yan siyasa na duniya suka mallaki kudade da kaddarori a asirce.
A Najeriya an gano cewa akwai wasu makusantan shugaba Buhari a cikin badakalar, gami da wasu fitattun ‘yan siyasa na kasar da suka hada da Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu da tsohon Gwamnan Anambra Peter Obi da sauran fitattun ‘yan kasar da aka bayyana sunayensu a cikin takardun Pandora da suka bankado yadda attajirai da ‘yan siyasar duniya suka mallaki haramtattun dukiyoyi a kasashen ketare tare da kauce wa biyan haraji.
Baya ga Bagudu da Obi, har ila yau tonon sililin ya ambato sunan tsohon wani Alkalin Alkalai na kasar da wasu tsoffin ‘yan siyasa da wani fasto da dai sauransu.
Sai dai wani abu wanda yafi daukar hankali a cikin wannan batu shi ne, yadda aka sami Bello Koko a cikin wannan harkalla, wanda shi ne mutumin da shugaba Buhari ya amince da shi, kuma ya mika masa shugabancin riko na hukumar tasoshin jiragen ruwa ta Najeriya, bayan sauke Hadiza Bala Usman, inda rahoton ya ce an samu maka-makan gidaje da Bello Koko yake ta sayewa a birnin Landan na kasar Burtaniya.
Yanzu haka kungiyoyin fararen hula da wasu masu ruwa da tsaki a Najeriya na kiran shugaba Buhari da ya bada umarnin tuhumar wadannan fitattun mutanen da aka ambata a 'Pandora Papers, ganin yadda gwamnatin take ikirrin yaki da cin hanci da rashawa.
Mai magana da yawun Buhari Garba Shehu yaki cewa uffan a lokacin da aka nemi jin ta bakinsa, inda ya ce a tuntubi hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ko kuma bangaren shari'a na kasar.
342/