Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kafafen yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa, arangamar ta yi sanadiyyar kashe mambobin kungiyar ta masu dauke da makamai su 4 da kuma wani jami'in tsaron gwamnatin Sudan guda daya, yayin da wasu majiyoyin suka bayar da rahoton kame wasu 'yan ta'adda 4.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, wata kungiyar ta'addanci ta kashe mambobin hukumar leken asirin Sudan 5 a makon da ya gabata, kafin jami'an tsaron su samu nasarar kame mambobinta a wani lokaci.
A cikin lokutan baya-bayan nan dai kasar tana fusakantar matsaloli masu tarin yawa na cikin gida, baya ga matsaloli na siyasa da suka dabaibaye kasar, tun bayan da sojoji suka dare kan mulki, bayan hambarar da gwamnatin Umar Hassan Albashir da mutanen gari masu zanga-zanga suka yi.
342/