3 Oktoba 2021 - 15:03
​Hamas A Shirye Take Ta Yi Musayar Fursinoni Da Isra’ila

Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta Falasdinawa ta bayyana cewa a shirye take ta yi musayar fursinoni da haramtacciyar kasar Isra’ila idan an sami mai shiga tsakani.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Cibiyar watsa labarai ta Falasdinawa ta nakalto Zaahir Jabbarin wani mai magana da yawun kungiyar ya na fadar haka a jiya Asabar.

Jabbarin ya kara da cewa kungiyar Hamas za ta yi musayar fursinoni da HKI ne kawai tare da cika sharuddanta, sannan tare da shiga tsakani na duk wanda kungiyar ta tabbatar zai iya aikin musayar fursinonin kamar yadda take so.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu dai fursinoni falasdinawa 4,850 ne suke tsare a cikin gidajen yarin yahudawan sahyoniyya daban-daban, sannan daga cikinsu akwai mata 41, yara matasa 225 da kuma wasu 250 wadanda har yanzun yahudawan basu tantance irin laifuffukan da suka yi masu ba.

342/