29 Satumba 2021 - 15:43
Jagora Ya Nada Peyman Jebelli A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gidan Rediyo Da Talabijin Na Iran (IRIB)

Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Sayyid Ali Khamenei ya nada Peyman Jebelli a matsayin sabon shugaban hukumar gidajen rediyo da talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB).

A cikin sanarwar da aka fitar ranar Laraba, Ayatollah Khamenei ,ya godewa shugaban IRIB mai barin gado Abdulali Ali-Asgari saboda "kwazonsa" tare da fatan samun nasara ga sabon shugaban hukumar Jebelli a sabon mukaminsa.

Ayatollah Khamenei ya fada a cikin sakon da ya aike wa Jebelli, "Na nada ka a matsayin shugaban wannan hukuma na tsawon shekaru biyar," in ji shi.

"Kafofin watsa labarai na kasa wata jami'a ce don habaka matakin wayar da kan jama'a da ilmi, kuma dandali ne mai fa'ida ga idanun kowa.

" Al'adu, karfafa ruhi, juyin juya hali, wanzar da Musulunci da Iran, da habaka hadin kai na kasa, suna daga cikin manyan abubuwan da yakamata a cimma ta hanyar ingantattun shirye-shirye masu nagarta" inji Imam Khamenei.

Jebelli, wanda aka haifa a shekarar 1967 a Tehran, malamin jami'a ne kuma babban masani kuma manazarci kan al'amuran siyasa.

Ya yi aiki a matsayin babban jami'i na hukumar radiyo da talabijin ta Jamhuriyar Musulinci ta Iran (IRIB World Service) tun daga ranar 14 ga Agusta, 2016.

An haifi sabon shugaban na IRIB a unguwar Shemiran ta arewacin Tehran, kuma yana magana da yaren Larabci mai kyau baya ga harshen Farisanci.

A cikin shekarunsa na hidima a cikin IRIB, Jebelli ya jagoranci fannoni daban -daban na aikin jarida da watsa labarai na talabijin, da watsa shirye -shirye.

Jebelli ya sami digirinsa na biyu a kimiyyar Musulunci daga Jami’ar Imam Sadik ta Tehran a 1993, kuma ya kammala jami’a a 2004 da digirin digirgir a fannin al’adu da sadarwa.

Ya rike mukamai da dama a sashin siyasa na IRIB, kuma ya koyar da dalibai da dama kan mukamai daban -daban a gidan talabijin na Iran.

Kafin nadinsa a matsayin shugaban IRIB World Service, ya kasance mamba a jami'ar IRIB, daraktan editan labarai a tashar IRIB TV2, babban daraktan labarai na cikin gida a kamfanin dillancin labarai na IRIB, babban daraktan na Tashar Talabijin ta Larabci ta Iran Al Alam, da kuma daraktan ofishin tashar Al Alam TV a Beirut.

Jebelli ya kuma yi aiki a matsayin daraktan watsa labarai na Majalisar Tsaron Kasa ta Iran a karkashin tsohon sakatarensa Saeed Jalili.

Bugu da kari, ya kasance Shugaba na Press TV, gidan talabijin na Ingilishi mallakin Iran mai watsa shirye shirye ba dare ba rana.

Har ila yau, ya yi zama jami'in diflomasiyya, inda ya yi aiki a matsayin jakadan Iran a Tunisia daga shekarar 2011 zuwa 2014.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen kaddamar da kamfanin dillancin labarai na bidiyo na Iran Press, gidan talabijin na Al Alam Syria da tashoshin talabijin na Intanet Hausatv da Press TV French.

342/