22 Satumba 2021 - 16:17
Gwamnatin Sudan Ta Ce Komai Ya Lafa A Yanzu

Hukumomi a Sudan sun tabbatar da cewa komai ya lafa bayan wani yunkurin juyin mulki a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa, ita ke rike da iko kan yanayin tsaro a birnin Khartoum, bayan ta bankado wani yunkurin juyin mulki.

Rahotanni daga babban birnin kasar wato Khartoum da kuma Omdurman na cewa an baza sojoji kan titi an kuma rufe gadojin da ke mahadar kogin Nilu.

Shekaru biyu da suka wuce ne a ka kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Albashir, sannan a ka kafa gwamnatin riko da ta kunshi sojoji da fararen hula.

Tunda farko dai Kakakin gwamnatin Sudan, kuma ministan labaran kasar Hamza Baloul Al-Amir ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an bankado yunkurin wani rukunin sojojin tsohuwar gwamnatin kasar na juyin mulki, kuma tuni aka katse hanzarinsu.

Ministan ya kuma sanar da kame shugabannin da suka yi yunkurin, yana mai cewa, yanzu haka ana gudanar da bincike bayan dakile yunkuri na karshe a sansanin sojojin dake yankin Alshara.

342/