Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A taron ne aka amincewa iran ta zama mamba na 9 a cikin kungiyar bayan kasashe 8 wadanda suke cikinta suka amince da hakan.
Wasu masana sun bayyana cewa zama mamaba na dindin din a cikin kungiyar SCO Iran ta sami wata dama ta kyautata dangantaka da wadannan kasashe da kuma kyautata tattalin arzikin kasarta.
Banda haka shugaban ya halarci taro na kasashen yankin dangane da kasar Afganistan, inda kasashen suka cimma matsayi na taimakawa mutanen kasar Afganistan da kuma bukatar a kafa gwamnatin hadin kan kasa wacce za ta samarda wakilci ga dukkanin kabilun kasar.
342/