18 Satumba 2021 - 12:20
Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Isa Conakry Don Ganawa Da Sojoji Masu Juyin Mulki

Shugaban kasar Ivory Coast Alassan Watara wanda ya jagoranci tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS zuwa kasar Guinea ya isa birnin Conakry a jiya jumma, kuma shugaban sojoji masu juyin mulki Mamady Dumboya ne ya tarbe shi bayan saukarsa a birnin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya ce a ranar Alhamis da ta gabace ce kungiyar ECOWAS ta gudanar da taron gaggawa a birnin Accra na kasar Ghana, dangane da juyin mulki na kasar Guinea inda ta dorawa sojojin da suka jagoranci juyin mulkin takunkuman tattalin arziki, sannan ta bukace su da su gudanar da zabe cikin watannin 6 su mikawa fararen hula shugabancin kasar.

Har yanzun dai sojoji masu juyin mulkin basu maida martani ba, kuma Mamady bai bayyana lokacin da za su maida mulki ga hannun fararen hula ba. Anna a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, sun yi ta ganawa da ‘yan siya, malaman addinin da kungiyoyi daban-daban a shirinsu na maida mulki ga fafaren hula bayan juyin mulki na ranar 5 ga watan Satumba.

342/