Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya bayyana cewa shekaru 2 kenan bayan da masu zanga-zanga suka tilasta masa sauka kan kujerar shugabancin kasar, wanda ya share shekaru kimani 20 yana kansa, AbdulAziz ya mutu.
Buteflika dai ya na daga cikin wadanda suka jagoranci samun ‘yencin kasar Aljeriya a shekara ta 1962 daga hannun turawan faransa ‘yan mulkin mallaka, a lokacin yana dan shekara 19 a duniya.
Buteflika ne ministan matasa na farko bayan samin ‘yencin kai ya na dan shekara 25 a duniya, sannan daga baya ya rike kujerar ministan harkokin wajen kasar.
Banda haka ya taba zama shugaban babban zauren MDD inda ya bawa shugaban kungiyar PLO na lokacin Yasir Arafat damar jawabi a majalisar, wanda kuma ya budewa falasdinawa kofar amincewa ta kasa da kasa.
An zargi jami’an gwamnatin Buteflika da cin hanci da rashawa bayan an tilasta masa sauka daga kan kujerar shugabancin kasar a shekara ta 2019 bayan yayi wa’adi har hudu. A halin yanzu kaninsa Sa’id Buteflika ya na cin kaso na shekaru 15 saboda cin hanci da rashawa.
342/