18 Satumba 2021 - 09:57
Ramedani: Ana Ganin Ruhin Tauhidi A Cikin Al'amuran Arbaeen / Ashura Ta Kasance Arangama Tsakanin Bangren Hankali Da Bangren Jahilci

Babban Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya ce: Maziyarci kan tafarkin aikin ziyarar ta Arbaeen, daga taki bayan taki zai iya kula da riskar sirruka na Allah, ana iya ganin ruhin tauhidi a cikin abin da ke faruwa Arbaeen.

Kamar yadda amfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) -ABNA , ya fitar an gudanar da taron Majalisar Ahlulbaiti (AS) ta duniya tare da jerin gwanon Arbaeen na masu fafutuka a fagen kasa da kasa kafin azahar yau, Alhamis, 16 ga Satumba 2021, a zauren taro na wannan majalisar dake Qom.

Ayatullah "Reza Ramezani" Babban Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) a wannan taron, yayin da yake ishara da bukatar kula da yanayin karfin da Arbaeen ke dashi, ya ce: Bai kamata mu rika yiwa Arbaeen kallon wasa ba, yakamata a san Majalisin Imam Husaini ( AS) yana da ayyuka a fannoni daban -daban, musamman yana da manufofi da al'adun da ba mu saba amfani da su ba, ziyarar Arbaeen ya kamata a dauke ta kamar Majalis din Imam Husaini (AS) a matsayin wani babban lamari a bangarori daban -daban, domin lamarin Arbaeen zai iya zama silar shiryar da mu bisa girman da yake da.

Ya ci gaba da cewa: "Arbaeen tana da damammaki da yawa, ta bangaren da suka shafi tausayawa da jinkai waɗannan su na daga cikin manyan halayen Arbaeen. Mutum ba zai iya samun abin da ya fi motsa zuciya fiye da labarin baƙin ciki na Karbala ba, wanda ke haifar da juyi na cikin jiki, wanda zai sa riskar girman Arbaeen, yanayin ɗabi'ar ta da Kuma halayyar ta.

Babban Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: An ambaci lada da yawa dangane da Ziyarar Arbaeen kuma Ma’nawiyyar Ubangiji tana bayyana a cikinsa, kuma maziyarci kan tafarkin ziyarar Arbaeen mataki -mataki zai iya kula da sirrin Allah dake tattare da hakan, zai iya riskar ruhin tauhidi a cikin yanayin Arbaeen. Idan da ace Korona ba ta yadu ba, to da an yi Arbaeen mafi ɗaukaka shekara bayan shekara na gaba.

Ayatullah Ramezani ya dauki Imam Husaini (AS) a matsayin cikakken abin koyi kuma ya bayyana cewa: Ashura ita ce fito na fito tsakanin bangaren hankali da bangaren jahilci kuma ginshikin kyawawan dabi'u a bangare daya kuma bangaren munanan dabi'u, A yayin makokin Hosseini, jinkai, sosa rai da hankali suna tare duka a waje daya.
Ya ci gaba da cewa: Akwai fuskoki dabam dabam dangane da Arbaeen wanda ya kamata agansu a tare waje guda.
Babban Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: Ziyarar Ashura yana karantar da mu mukamai 20 kamar mukamin wilaya da na kusanci a tafarkin tafiya.

Ayatullah Ramezani yana ganin ya zama dole a kula da yanayin damar maki na Arbaeen kuma ya fayyace cewa: ya kamata a mai da hankali sosai ga waɗannan halayen, waɗanda mafi yawansu suna cikin girman ilimi, tarbiyya, zamantakewa da siyasa. Abin takaici, mun yi sakaci da yanayin siyasar Arbaeen kuma ba mu mai da hankali sosai gare ta ba.
Ya ci gaba da cewa: "Bangaren kasa da kasa, ya kamata a kara mai da hankali kan lamarin Arbaeen." Tabbas, gwargwadon ƙarfin iya abin da aka yi to gwargwadon ƙaruwa hakan, da samun mafi girman canji a ciki.
Babban Sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya yi nuni da cewa: Dole ne mu yi amfani da damarmakin Arbaeen a fannoni daban-daban.

342/