15 Satumba 2021 - 11:13
​Siriya: Shugaba Assad Ya Kai Ziyarar Ba Zata Kasar Rasha

Shugaban kasar Siriya Bashar Asad ya kai ziyarar ba zata kasar Rahsa a jiya Litinin, inda ya gana da Vladimir Putin shugaban kasar ta Rahsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shuwagabannin biyu sun gana a fadar Crimlin, inda shugaban Putin ya taya shi murnar sake zabensa kan kujerar shugabancin kasar Siriya a cikin zaben watan mayun da ya gabata.

Putin ya kara da cewa matsalar kasar Siriya ita ce samuwar sojojin kasashen waje a kasar Siriya ba tare da izin mdd ko kuma gwamnatin kasar Siriya ba.

Shugaban ya kara da cewa har yanzun akwai ragowar ‘yan ta’adda a yankunan da suke karakshin sojojin mamaya, kuma banda haka suna ci gaba da cutar da mutanen yankin.

Amurka da kawayenta sun mamaye wasu yankunan a arewacin kasar Syriya tun shekara 2014 da sunan yaki da ta’addanci, amma a halin yanzu su ne suke goyon bayan ‘yan ta’addan da suka rage a arewacin kasar ta Siriya.

342/