5 Satumba 2021 - 10:08
​Lebanon: Mutane Suna Maraba Da Shirin Iran Na Wadata Kasar Da Makamashi

Daruruwan mutanen kasar Lebanon ne suka taru a kusa da tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut, domin nuna farin cikinsu da da shirin Iran na wadata kasar da makamashi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Rahotanni daga birnin Beirut na kasar Lebanon na cewa, a yau Asabar daruruwan mutane sun taru a kusa da tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut, domin nuna farin cikinsu da shirin Iran na aike wa da katafaren jirgin ruwa da yake dauke da makamashi zuwa kasar ta Lebanon.

Rahoton ya ce wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jirgin na Iran wanda yake dauke da makamashi yake kan hanyarsa ta isa gabar ruwan Beirut, bayan da ya yada zango a gabar ruwan kasar Syria.

Kasar Lebanon dai ta shiga cikin matsanancin hali sakamakon rashin makamshi, bayan da Amurka da wasu kasashen turai suka dauki matakin takurawa kasar, da nufin ganin sun raunana kungiyar Hizbullah, wadda suke kallonta a matsayin babbar barazana ga gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Sakamakon rashin makamashi, ana fuskantar gagarumar matsala musamman asibitoci da wuraren kiwon lafiya, kamar yadda hakan kuma ya shafi rayuwar jama’a kai tsaye a kasar ta Lebanon, wannan kuma gwamnatin kasar ba za ta iya shigo da makashin daga waje ba.

Wannan ne yasa kungiyar Hizbullah ta yanke shawarar shigo da makashi daga kasar Iran, day a hada da manfetur da dangoginsa, inda yanzu haka katafaren jirgin ruwa na Iran dauke man fetur ad dangoginsa ke gab da isa birnin Beirut, sanna kuma wasu jiragen za su taso daga Iran zuwa Lebanon nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

342/