Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : hafin yanar gizo na labarai ‘Africanews’ ya nakalto kakakin gwamnatin jihar Naje Ahmed Matane yana fadar haka, ya kara da cewa daga yanzu an dakatar da kasuwar dabbobi na mako-mako a jihar sannan an haramta saida man fetur a cikin jereka a gefen tituna, har zuwa abinda hali ya yi.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin jihar ta Naje ta ha na a sayarwa ababen hawa man fetur sama da naira dubu 10,000.
Gwamnatin ta kammala da cewa, ta dauki wadannan matakan masu tsauri ne, duk da cewa ta takurawa mutane, amma ta na son hana ‘yan bindiga ma su sace ‘yan makaranta cin kerensu ba babbaka wajen haddasa fargaba da tsaro a cikin zukatan mutane, da kuma satar ‘yan makaranta.
Kafin haka dai jihohin Katsina, Kaduna Da Zamfara sun dauki irin wadannan matakan a jihohinsu.
342/