Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na labarai ‘Africanews’ ya kara da cewa ministocin harkokin waje na kasashen Cadi, Nijer, Tunisiya, Sudan, Masar da Aljeriya ne suka halarci taron na kwanaki biyu a birnin Aljies na kasar Aljeriya.
Har’ila yau, Jan Kubis wakilin MDD na musamman a kasar Libya da babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Ahmed Aboul Gheit da kuma wakili daga kungiyar tarayyar Afrika ma sun sami halattan taron.
Tun shekara ta 2011 kungiyar tsaro ta NATO ta tallafawa yan tawaye suka kifar da gwamnatin Mu’ammar Kazzafi , wanda ya daga karshe ya kai ga barkewan yaki a kasar.
Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekarar da ta gabata, a lokacinda aka sasanta tsakanin mutanen kasar sannan aka kafa gwamnatin rikon kwarya.
342/