29 Agusta 2021 - 10:25
Iran : Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ne Ke Da Alhakin Samar Wa Kansu Tsaro

Sabon ministan harkokin wajen kasar Iran, Amir-Abdollahian, ya bayyana bukatar samar da tsaro mai daurewa a yankin tare da hadin guiwar dukkan kasashen yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Mista Abdollahian, ya kuma bayyana cewa ba yadda za’a samu tsaro a yankin muddin kasashen ketare na shishigi a al’amuran da suka shafi yankin gabas ta tsakiya.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya bayyana hakan ne yayin taron kasa da kasa na Bagadaza, mai manufar kwantar da hankali a yankin.

Ya kara da cewa Jamhuriyar musulinci ta Iran, har kulun tana bukatar samar da zaman lafiya a yankin ta hanyar tattaunawa, tare da fatan kasashen yankin zasuyi Magana da murya guda game da batun tsaro cikin aminci da yarda, da karfafa alaka ta makobtaka mai kyau amma ba tare da shishigi na kasashen ketare ba.

Amir-Abdollahian, ya kuma yabawa Iraki game da kokarin ta na samar da zaman lafiya a yankin ta hanyar shirya wannan taron, tare da jaddada goyan bayan Iran ga mahukuntan na Bagadaza game da wannan batu.

342/