20 Agusta 2021 - 15:13
An Gudanar Da Zaman Makoki Na juyayin ranar Shahadar Imam Hussain A kasar Iran da ma Sassa daban-daban na duniya

Miliyoyin Alumma musulmi mabiya mazhabar Ahlul baiti a fadin duniya ne suka gudanar da zaman makoki na juyayin zagayowar ranar 10 ga watan Muharram na shahadar Imam Hussaini limami na 3 daga cikin limaman shirrya 12 na iyalan gidan manzon Allah tsira da aminci su tabbata gareshi da alayensa tsarkaka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Kuma ana wannan zaman makokin ne don tunawa da rana ta 10 ga watan Muharram ranar da Imam hussaini jikan manzon Allah yayi shahada a filin karbala tare da sahabban sa guda 72, a shekara ta 680 bayan hijira, bayan da suka yi yaki na jarumtaka da dubban dakarun Yazidu dan Mu’awiya, domin kalubalantar zalunci da rashin Adalci da gwamnatin yazidu ke nunawa

A kasar Iran an gudanar da zaman makokin ne cikin yanayi na bada tazar tsakanin mutane don hana yaduwar Cutar Korona Virus, da ta yi kamar a kasar,

A kasar Pakistan kuwa an kai hari ne kan masu zaman makokin a lardin Punjab dake gabashin kasar da hakan ya haddasa mutuwar mutane 5 tare da jikkata mutane 50 Da suka ha da yara kanana, sama da mutane 400 ne suka halarci wajen makokin na tunawa da shahadar Imam Hussain As, Tuni dai aka yi tir da wannan hari na rashin tausayi.

342/