ABNA24 : Zarif ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manzon babban sakataren MDD na musamman kan lamurran Afghanistan Jean Arnault wanda a halin yanzu ya ke ci gaba da ziyarar aiki a nan Tehran don tattaunawa da jami’an ƙasar kan yanayin da ake ciki a ƙasar ta Afghanistan.
Yayin da ya ke magana kan mummunan yanayin da Afghanistan ɗin take ciki, Zarif ya ce siyasar kuskure da manyan ƙasashen duniyan suka ɗauka a Afghanistan suna daga cikin abubuwan da suka haifar da halin da ake ciki a halin yanzu a ƙasar.
Don haka sai ministan harkokin wajen na Iran ya ce wajibi ne ƙasashen duniya su ɗau matakan da suka dace wajen goyon bayan tattaunawa da kuma magance rikicin da ke faruwa a Afghanistan ɗin ta hanya ta siyasa da kuma yin Allah wadai da duk wani tashin hankali da kuma amfani da ƙarfi a ƙasar.
Babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya sake jaddada ƙudurin Iran na taimakawa wajen tattaunawar da ɓangarori daban-daban na Afghanistan ɗin suke yi don cimma zaman lafiya a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.
342/