8 Agusta 2021 - 20:06
​Aljeriya: Sanya Isara’ila A Cikin Kungiyar AU Zai Raba Kan Kungiyar

Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ramadan Lamamra ya bayyana cewa aikin shugaban harkokin gudanar na kungiyar Tarayyar Afirka Musa Fakih Muhammad na karbar Isra’ila a matsayin mamba mai sanya ido a cikin kungiyar zai raba kan kungiyar ne kawai.

ABNA24 : A wata tattaunawa da jiridar “Afajir” ta kasar Aljeriya Lamamra ya bayyana cewa idan Fakih ya dage kan shigar da Isra'ila a cikin kungiyar AU, ba abinda hakan zai jawo in banda rarrabuwar kai a tsakanin kasashen kungiyar .

Ministan ya kara da cewa uzurin da Musa Fakih ya bayar kan abin da yasa ya amince da karbar Isra'ila a cikin kungiyar AU a matsayin mamba mai sanya ido a cikinta ba zai amfanar da komai ba.

Kuma gwamnatin kasar Aljeriya da sauran kasashen kungiyar ta suka bukaci a kori Isra'ila daga kungiyar zasu ci gaba da gwagwarmayansu na ganin an yi hakan.

A cikin makonnin da suka gabata ne Fakih ya bawa Isra'ila damar zama mamba a kungiyar ta AU ba tare da shawartar mafi yawan yayan kungiyar ba.

342/