5 Agusta 2021 - 11:49
Kasashen Duniya Sun Alkawarta Taimaka Wa Al’ummar Lebanon Da Dalar Amurka Miliyan 370

Kasashe mahalarta taron kasa da kasa domin taimakawa kasar Lebanon, sun alkawarta taimakawa al’ummar kasar Lebonon da Dalar Amurka kimanin miliyan 370.

ABNA24 : Bangarorin sun sanar da hakan ne a karshen taron da suka gudanar ranar Laraba wanda kasar Faransa da MDD suka shirya.

Kasar Faransa ta ce za ta taimakawa al’ummar Lebanon da Yuro miliyan 100, yayin da kuwa Amurka ta ce za ta taimakawa da sabon tallafin jin kai na Dala miliyan 100.

Saidai mahalarta taron sun bukaci kafa gwamnati a kasar ta Lebanon domin ceto kasar, tare kuma da bayyana damuwarsu kan jinkirin da ake samu wajen gudanar da bincike kan musababin fashewar data auku yau da shekara guda a tashar ruwan Beirut.

Fashewar wacce ta auku a ranar 4 ga watan Agustan 2020, ta yi sanadin mutuwar mutum 191 tare da jikkata wasu 6,000 a alkalumman da hukumomin kasar suka fitar a watan Satumban bara.

An bayyana cewa fiye da tan 2,750 na wasu sinadirai na Ammonium nitrate da aka ajiye a wani wajen ajiye kayayyaki na tsawon shekaru shida ne ya janwo wannan barna.

Aukuwar lamarin dai ya kara jefa kasar cikin matsin tattalin arziki da rikicin siyasa da ba’a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar.

342/