ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto jami’i mai kula da al’amuran watsa labarai na ofishin jagoran ya na fadar haka a yau Asabar.
Kafin haka dai Alkalin alkalan kasar Iran Gholam-Hossein Mohseni-Ejei ya rubutawa Imam Khamenei wasika inda a cikinta, ya bukaci jagoran ya yi rangwame ko ya yafewa fursunoni 2,825 hukuncin da aka yanken masu a kutuna daban-daban na kasar saboda zagayowar wadannan kwanaki farinciki masu alfarma.
342/