30 Yuli 2021 - 14:10
​An Gudanar da Tarukan Idin Ghadir Na Kasa Da Kasa

An gudanar da tarukan ranar Idin Ghadir na kasa da kasa tare da halartar masana daga kasashen duniya daban-daban.

ABNA24 : A kasar Afirka ta kudu an shirya zaman taron ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, wanda malamai dam asana daga kasashen duniya daban-daban suka halarta, kuma suka gabatar da kasidu dangane da matsayin wannan rana ta Ghadir a jiya Alhamis.

Daga cikin wadanda suka halarci tarukan, akwai wakilan cibiyoyi na addini na kasar da kuma na wasu kasashe da suka hada hard a Amurka Burtaniya Canada da sauransu, da kuma wasu daga cikin kasashen Afirka da na Asia da kuma Latin Amurka gami da kasashen larabawa.

A kasar saudiyya ma an an gudanar da irin wadannan taruka na ranar Idin Ghadir a garin Qatif da ke gabashin kasar.

Wannan taro dai yana daga cikin muhimman taruka da mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) suke gudanarwa a ko'ina a cikin fadin duniya, domin tunawa da ranar jawabin karshe da manzon Allah (SAW) ya yi bayan kammala aikin hajjin bankwana.

A bisa ruwayoyi da sahabbai 115 suka ruwaito wanda hakan yasa ruwayar ta zama a matsayin tawatur saboda ingancinta,a ranar ne Manzon Allah (SAW) ya bayyana dan uwansa kuma surukinsa kuma sahabinsa Imam Ali (AS) a matsayin majibincin lamarin muminai a bayansa.

Mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar Saudiyya wadanda su ne kashi 15 na al'ummar kasar suna gudanar da irin wadannan taruka na tunawa da wannan rana a yankunansu da suke gabashin kasar.

342/