26 Yuli 2021 - 16:42
Somalia : An Jinkirta Zaben Sanatoci Da Aka Shirya Yi Ranar Lahadi

Bayanai daga Somalia, na cewa an jinkirta zaben sanatoci da aka shirya gudanarwa yau Lahadi, a wannan kasa data shafe watanni tana fama da rikicin siyasa.

ABNA24 : Tuni dai lamarin ya sanya rudani a kasar dake yankin kahon Afrika.

A jadawalin zaben kasar, yau 25 ga watan Yuli, ne aka tsara gudanar da zaben wanda za’a shafe dogon lokaci ana gudanarwa har zuwa ranar 10 ga watan Oktoba inda za’a karkare da zaben shugaban kasa.

Rashin bada sunayen ‘yan takara a zaben, da batun kafa kwamitoti na yankuna wadanda zasu kada kuri’a shi ne ya haifar da jinkirta zaben, a cewar wasu majiyoyi daga gwamnati.

Shi ma da yake tabbatar wa kamfanin dilancin labaren AFP, hakan, kakakin gwamnatin Somalia, Mohamed Ibrahim Moalimu, ya ce an jinkirta zaben amma ana ci gaba da shirye shiryen zabukan.

A watan Afrilu, da ya gabata, batun tsawaita wa’adin shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda ya kare a ranar 8 ga watan Fabarairu, ya janyo dauki ba dadi sosai a Mogadisho babban birnin kasar.

342/