13 Yuli 2021 - 11:09
Gaza: UNICEF Ta Ce Kananan Yara Miliyan Guda Na Buƙatar Agajin Gaggawa

Hukumar Kula Da Кananan Yara Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta buƙatar da a aike da agajin gaggawa zuwa ga Zirin Gaza da yahudawan sahyoniya suka killace shi, tana mai cewa akwai kimanin ƙananan yara miliiya ɗaya da suke buƙatar taimakon gaggawa.

ABNA24 : Hukumar ta UNICEF ta bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter inda tace: Gaza tana da ƙananan yara miliyan ɗaya waɗanda mafi yawansu suna buƙatar taimakon gaggawa. Don haka muna kiran da a kai musu ɗauki na gaggawa a ɓangarorin kiwon lafiya, ruwan shad a kuma ilimi.

Tsirin na Gaza dai wanda ya ke da mutanen da suka kai miliyan biyu ya kasance ƙarƙashin killacewar ‘Isra’ila’ tun watan Yunin 2007 shekaru biyu bayan da Isra’ilan ta janye daga mamayar da ta yi wa Zirin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ma dai babbar jami’ar agaji ta MDD a yankin Falastinu Lynn Hastings ta ja kunnen cewa ci gaba da killace Zirin da Isra’ila take yi na sanya ɓangarori masu muhimmanci da suke kula da rayuwar mutane a yankin cikin hadari.

A kan haka ta buƙaci Isra’ilan da ta sassauta killacewar da ta yi wa Zirin Gaza don a samu damar shigar da kayayyakin agajin da ake buƙata na gaggawa don ceto rayukan wani adadi mai yawa na al’ummomin yankin.

342/