ABNA24 : Jaridar Egypt daily ta nakalto ministan harkokin shige da fishe na kasar ta Masar, Nabila Makram ta na cewa gwamnatin kasar ta sami hadin kai da wasu kamfanonin safara 38 don kwaso ‘yan kasarta wadanda suka makale a tashoshin jiragen sama a UAE.
Ministan ta kara da cewa an sami hadin kai daga ma’aikatu daban-daban don samun damar dawo da wadannan ‘yar kasarta daga UAE.
Gwamnatin kasar Saudia dai ta dauki wannan matakin dakatar da tashin jiragen saman kasarta zuwa ko kuma kawo fasinjoji daga wadan nan kasashe ne ne saboda hana cutar korona shigowa kasar.
Labarin ya kara da cewa mai yuwa fasinjojin da za’a dauko daga UAE wadanda kuma suka fito daga inda ake fama da annobar koronan su shigo da ita kasar.
Ministan ta kammala da cewa wasu ‘yan kasar 403 sun zabawwa kansu wasu hanyoyin don radin kansu na komawa gida.
342/