ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Mehra na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Iran a MDD ya na fadar haka a safiyar yau Asabar.
Kazem Gharibabadi ya kuma kara da cewa, Aparo Massimo mataimakin shugaban hukumar ta IAEA zai ziyarci Tehran ne duk tare da cewa ba’a shirya wata ganawa da shi a can ba.
Kasar Iran dai ta takaita ayyukan sanya ido na hukumar ta IAEA a kan ayyukanta na makamashin nukliya ne, don zargin hukumar tana da hannu wajen taimakawa Isara’ila a hare haren da ake kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar.
A halin yanzu dai tattaunawa ta komawar kasar Amurka cikin yarjejeniyar ta JCPOA ta cije saboda Amurka ta ki ta amincewa da wasu bukatun kasar ta Iran dangane da komawar.
342/