3 Yuli 2021 - 13:05
​Sarkin Jordan Ya Taya Zababben Shugaban Kasar Iran Murna

Sarkin kasar Jordan ya aike wa zababben shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim ra’isi da sakon taya murna.

ABNA24 : Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin sakon wasikar da sarkin kasar ta Jordan Abdullahi na biyu ya aike wa Sayyid Ibrahim Ra’isi, ya taya shi murna dangane da nasarar lashe zaben shugaban kasa da ya yi.

Baya ga haka kuma sarkin kasar ta Jordan ya bayyana wa Ra’isi cewa, Jordana shirye take ta kara karfafa alakarta da kasar Iran a bangarori daban-daban, domin al’ummomin kasashen biyu su ci gajiyar alakar da ke tsakaninsu.

Haka nan kuma ya yi fatan alhairi ga kasar ta Iran da dukkanin al’ummominta, da samun ci gaba a dukkanin bangarori fiye da kowane lokaci a baya.

Kasar Jordan na daga cikin kasashen larabawa da suke da kyakkyawar alaka da kasar ta Iran.

342/