ABNA24 : Shafin yada labarai ta ‘Africanews’ ya nakalto Yasuhiro Yamashita ya na fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa za su kara daukar matakai ma su tsanani a tashoshin jiragen sama na kasar don tabbatar da cewa ba wanda ya shigo da kwayar cutar cikin kasar daga cikin tawagogin da suka fara isowa daga kasashen duniya daban-daban.
Kafin haka dai a ranar lahadin da ta gabata ce aka tabbatar da cewa mutane biyu daga tawagar kasar Uganda da ta isa kasar sun kamu da cutar, wato wani Koci da kuma dan wasa guda.
Labarin ya bayyana cewa an kebance tawagar ta kasar Uganda da kuma mutane biyu da suka kamu da cutar bayan isowarsu birnin Tokyo a ranar.
Yamashita ya ce akwai yiyuwan wanda ya yi alluran riga kafin cutar ta Covid 19 har sau biyu ma, ya kamu da cutar, don haka ba zasu yi wasa ba, wajen tabbatar da cewa duk wanda ya shigo kasar an gwada shi.
342/